A jiya Alhamis ne dai gwamnatin kasar ta Uganda ta sanar da cewa; Za ta farfado da tsohuwar shawarar yi doka da aka taba bijiro da ita a kasar, wacce ta tanadi zartar da hukuncin kisa akan wadanda aka samu da neman jinsin guda

Ministan kyawawan al’adu da kare mutunci na kasar ta Uganda Simon Lokodo ya ce; Neman jinsi guda ba tabi’ar mutanen kasar Uganda ba ce,amma a cikin shekarun bayan nan masu wannan mummunar tabi’a, suna jan hankalin dalibai a makarantu, musamman matasa don haka dole a takawa lamarin birki.

Minstan kyawawan al’adu da kare mutunci na kasar ta Uganda ya cigaba da cewa; A halin da ake ciki a yanzu dokokin kasar sun takaita da daukar neman jinsi guda a matsayin babban laifi, wanda bai wadatar ba,don haka ya kamata a rika zartar da hukuncin kisa akan masu aikatawa.