A jiya talata 8 ga watan oktoba ne alummar kasar yamen a birnin Sana’aa suka gudanar da buki karo na 3 na zagayowar kisan kare dangi da kasar Saudaiya ta yi wa Alummar kasar Yamen,da ya jawo mutuwar sama da mutane 140, shekaru biyar kenan da kasar saudiya ta kaddamar da hare hare kan kasar Yamen da mafi yawancin yafi shafarfararen hula.

A wajen taron alummar kasar sun yi tir da ci gaba da kai hare hare kan fararen hula da kasar saudiya ke yi, kasar saudiya ta fara kai hari kan kasar Yamen ne tun a shekara ta 2015 da nufin dawo da gwamnatin tsohon shugaban kasar ta Yamen Abdu rabbuhu, amma har yanzu hakarta ba ta cimma ruwa ba, ban da kashe mata da yara kanana dalallata muhimman gine- gine na kasar.