Gwamnatin kasar Kenya ta bude layin dogo na jirgin kasa wanda ya lakume dalar Amurka biliyon 1.5, wanda kuma kasar Cana ta gina tsakanin birnin Nairobi babban birnin kasar da kuma garin Naivasha, wanda ake saran zai taimaka wajen jigilar kayayyaki da kuma mutane.

Kafin haka dai kasar Cana ta gida wani layin dogon wanda ya taso daga birnin Nairobi zuwa Mombasa na bakin ruwa a shekara ta 2017.

Shugaban kasar ta Kenya Uhuru Kenyata ne ya jagorancin bikin bude layin dogon wanda ya samu jinkiri kadan wajen kammala aikin nasa.