Babban kwamandan dakarun kare juyin juya halin musulunci na kasar Iran Manjo Janar Husain Salami ya yabawa hukumar gidajen radiyo da talabijin ta kasar Iran kan gagarumin kokarin da take yi don isar da gaskiya a ko ina a duniya, ya kuma kwatanta hukumar da rana, wacce, duk tare da kankantarta tana haska ko ina a duniya.

Janar Salami wanda ya gabatarwa da jawabi a wani taron girmamawasu yan jaridu na hukumar gidajen radiyo da talabijin ta kasar a dakin taro na hukumar da ke nan Tehran a yau Lahadi, ya kara da cewa gwamnatin kasar Amurka tana son mutanen duniya su ci gaba da kasancewa cikin duhu.

Dangane da lamuran da suka tafiya a duniya, amma duk tare da karancin kayan aiki da kuma kudade wanda hukumar IRIB ta ke fama das u, ta sami nasarori masu yawa wajen isar da gaskiya ga mutaneda dama a duniya.
Sh ma shugaban hukumar Abdol Ali Ali-Askari, a cikin jawabinsa a taron ya yi kira ga yan jaridu na hukumar da su yi kokarin gano irin hanyoyin da makiya suke bi wajen yakar kwakwalen mutane a duniya don fuskantarsu ta hanyoyin da suka dace.

KNPRSCD 08
Kaduna Press
Safwan Harun✍🏼