Kasar Koriya ta arewa ta sanar da gudanar da gwajin wani makami mai linzami a cikin nasara.

Tashar talabijin din kasar Koriya ta arewa ta bayar da rahoton cewa,ajiya dakarun kasar sun harba wani sabon makami mai linzami daga cikin jirgin ruwa mai tafiya karkashin ruwa (submarine) a cikin nasara.

Gwajin makamin dai na zuwa ne a daidai lokacin da ake sa ran za a koma tattaunawa tsakanin kasar da kuma Amurka kan shirinta na makaman nukiliya.

Wannan gawji dai ya bakanta ran Amurka, amma duk da haka gwamnatin kasar ta Amurka ta kirayi Koriya ta arewa da ta daina gudanra da irin wadannan gwaje-gwaje da ta kira na tsokana, ta rungumi hanyar tattaunawa domin kawo karshen takkadamar da ake yi kan makaman nukiliya da kasar ta mallaka.

A nasa bangaren shugaban kasar ta Koriya ta arewa Kin Jan Un ya nuna farin cikinsa maras misiltuwa kan nasarar da sojojin kasarsa suka samu wajen gwajin sabon makamain da kasar ta kera.