Dan Takarar shugabancin kasa karkashin Inuwar Jam’iyar PDP Atiku Abubakar ya daukaka kara ne zuwa kotun koli bayan da babbar kotun kasa a watan da ya wuceta yi watsi da karar da ya shigar na kalubalantar nasarar da aka sanarcewa dan takarar shugabancinkasar Muhammadu Buhari danjam’iyar APCya samu kuma shugabankasamai ci a yanzu a zaben da aka gudanar a farkon wannan shekarar da muke ciki.

Sha’ariar da ta gudana a yau a birnin tarayyar Abujawadda alkalin alkalai na kasa Mohammad Tanko ya jagorantashi da wasu alkalai 5 da suke mara masa baya, ta yi watsi da karar da Atiku shigar ta kalubalnatar takardar shedar kammala karatun sakandire ta mohammadu buhari, inda ya ce ta bogi ce don babu wata takarda makamancinta a lokacin da aka bayyana ya kammala karatu, da kuma zargin hukumar zabe ta kasar INEC da murda zaben domin bawa shugaban kasa mai ci a yanzu Nasara.

Sai dai alkalin kotun ya bayyana cewa a nan gaba za su bayyana dalilan da suka sa aka yi watsi da karar da Atikun ya shigar.