Cikin wani rahoto da ta fitar kungiyar kare hakin bil-adama ta kasa da kasa ta ce takunkumin da kasar Amurka ta kakabawa jamhoriyar musulinci ta Iran zai cutar da lafiyar fararen hula da dama a kasar

Kamfanin dillancin labaran Pars ya nakalto kungiyar kare hakin bil-adama ta kasa da kasa a jiya talata cikin wani rahoto da ta fitar na cewa takunkumin da kasar Amurka ta kakabawa jamhoriyar musulinci ta Iran zai takaita shigar da makunkunan da ake bukata sosai cikin kasar.

A yayinda gwamnatin Amurka ke riyar cewa ta bayar da damar a shigar da kayayyakin agajin cikin kasar ta Iran, kungiyar kare hakin bil-adama ta kasa da kasa ta ce kamfanonin samar da magani na kasashen Amurka da Turai, ba za su iya shigar da magani cikin kasar ta Iran ba, saboda takunkumin kudi da aka kakabawa kasar.

Sarah Leah Whitson babbar daraktar kungiyar kare hakin bil-adama ta yankin gabas ta tsakiya ta ce hukumomin birin Watsington na da'awar cewa suna tare da al'ummar Iran, amma a bangare guda girman takunkumin da aka kakabawa kasar na cutar da mafi yawan fararen hular kasar musaman ma a bangaren kiyon lafiya.

A bangare guda ministan harakokin wajen kasar Iran Muhamad Javad Zarif a ranar lahadin da ta gabata ya rubuta a shifnsa na twitter cewa kasar Amurka ta fitar da wani sabon makirci na tsananta takunkumin karya tattalin arziki na ta'addanci a kan jamhoriyar musulinci ta Iran.