A wani rahoton da kungiyar kare hakkin bil’adama ta Amnesty International ta fitar a safiyar ranar jumma’a, da ya gabata kungiyar ta ce gwamnatin kasar Turkiyya tana tilastawa yan gudun hijiran kasar Siriya kimani miliyon 3.6 wadanda suke cikin kasar komawa yankin da ta mamaye a arewacin kasar ta Siriya, duk da cewa har yanzun ba’a dakatar da yaki a yankin ba.

Gwamnatin kasar Turkiya a nata bangaren ta ce ya zuwa yanzu ta maida yan gudun hijira 350,000, tare da radin kansu zuwa yankin da ta kira tudun mun tsira a arewacin kasar ta Siriya.

Amma kungiyar Amnesty Inl. ta bayyana cewa, a binciken da ta gudanar ta gano cewagwamnatin Turkiyya tana tilastawa yan gudun hijiran amincewa da komawa yankin ne ba tare da sonsu ba.