Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

Kungiyar Boko Haram Ta Kashe Sojojin Najeriya 11A wani labarin da jaridar Premium times ta kasar Najeriya ta buga ta ambaci cewa; Baya ga kashe sojoji 11 da ‘yan kungiyar ta Boko Haram su ka yi, sun kuma jikkata wasu 14 a wani gumurzu da dakarun bataliya ta musamman ta 154 a yankin Mauli zuwa Borgozo.

An yi wannan fadan ne dai a ranar 3 ga watan nan na Oktoba, wanda kuma ya yi sanadin bacewar wasu Karin sojojin su biyu.

Bugu da kari ‘yan kungiyar ta BH sun kwashi ganimar bindigo samfurin AK47 guda 11 da kuma wata mota dake dauke da babbar bindigar garbo jirage.

Wannan sabon fadan dai yana zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin jahar Borno ta bai wa wasu mutane 30 kwangilar yin addu’oi a birnin Makka na Saudiyya, domin samun galaba akan kungiyar ta Boko Haram.

Post a Comment

0 Comments

Close Menu