Dubun dubatan magoya bayan kungiyar jihadi Islami a yankin zirin gaza ne suka fito kwansu da kwarkwatarsu domin gudanar da bukin cika shekaru 32 da kafuwa, ita dai kungiyar Jihadi Islami bata amince da HKI ba kuma tana gwagwarmayar kafa kasar Palasdinu mai cin gashin kanta ba karkashin mamaya da babakeren HKI ba.

Da yake bayani da dubban magoya bayansu ta hanyar tauraron dan adam babban magatakardar kungiyar JIhadil IslamiZeyadal-Nakhale ya jadda game da muhimmacin ci gaba da jajircewa a matsayin hanyar daya tilo ta kwatar yancinsu.

Dr Fathi Shakaki shi ne wanda ya kafa kungiyar Jihadil Islami da ya tasirantu da koyarwa wanda ya kafa Jamhuriyar musulunci ta Iran Marigayi Imam Khumaini yardarm Allah ta tabbata gareshi, kuma tana daga cikin jegon kungiyoyin gwagwarmyar nekan yanci a yankin na Palasdinu dake da bangaren soji Qudus Brigade,