Babban saktaren kungiyar Kasashen Larabawa ya yi tir da hare-haren da kasar Turkiya ke kaiwa kan arewacin kasar Siriya tare da neman kasar da tadakatar da kai harin.

Kafar watsa labaran Alyaumu-sabi’I ta ruwaito Ahmed Aboul Gheit babban saktaren kungiyar kasashen Larabawa a wani taro da suka yi jiya asabar ya yi tir da farmakin da Sojin Turkiya ke kaiwa kan al’ummar arewacin kasar Siriya tare da bayyana cewa kasar ta Turkiya na kokarin kawo wani gagarimin sauyi ga al’ummar wannan yanki.

Aboul Gheit ya bukaci kasar Turkiyar da ta janye sojojinta daga cikin kasar Siriya.

Har ila yaubabban saktaren kungiyar kasashen Larabawa ya ce kasar Turkiyan ta kaddamar da hari ne kan daya daga cikin kasashen Larabawa kuma hakan na nufin kaddamar da yaki kan kasashen Larabawa, don haka mahukuntan birnin na Ankara su dauki nauyin duk wani abinda zai biyo baya, sakamakon kai wannan hari.

Abu Ghait ya kara da cewa manufar Turkiya na kai wannan hari, shine raba yankin da kasar Siriya, sannan kuma ya bukaci kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya da ya dauki matakin gaggauwa na tilastawa Turkiya su dakatar da wannan farmaki.