wanann sanarwar tana zuwa ne yan kwanaki kafin cikar wa’adin da kungiyar kwadago ta kasa wato NLC a takaice, ta dibar ma gwamnatin Nigeria, da ta fara aiki da sabon tsarin biyan albashi ko kuma ta fuskanci yajin aiki na sai baba ta gani.

A wata takardar bayan taro da shuwagabannin kungiyar kwadago su ka fitar sun gargadi gwamnati na tsayar da harkar tattalin arzikin kasar cak nan da 16 ga watan Oktoban da muke ciki matukar ba ta fara aiki da fara biyan mafi karancin albashi da a aka cimma matsaya akai ba. Bangaren gwamnati da na kungiyar kwadago sun tattauna a lokuta daban -daban domin warware batun fara biyan mafi karanci albashi da ake takaddama akai.

Babbar matsalar da ta jawo rashin fara aiki da biyan mafi karancin albashin shi ne yanayin kason da za’a karawa ma’aikata a matakin albashi daban- daban, sai dai tuni aka fara biyan mafi karancin albashin ga ma’aikatar da suke mataki na 1-6.