Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

Kwamitin Tsaro Zai Yi Zama Kan Farmakin Turkiyya Kan Kurdawan Siriya


A yau Alhamis ne ake san kwamitin tsaro na MDD, zai yi zama, bisa bukatar kasar Faransa kan farmakin da Turkiyya ta kaddamar kan kurdawa Siriya.

A jiya ne kasar Turkiyya, ta kaddamr harin sama dana kasa kan kurdawan arewacin Siriya, da take dangantawa da ‘yan ta’adda.
Tuni dai kasashen duniya sukayi tir da matakin sojin na Turkiyya, tare da umartar ta data dakatar da farmakin.

Shugaban kwamitin kungiyar tarayya turai, Jean-Claude Juncker, ya bukaci Turkiyya ta dakatar da matakin, tare da yi mata barazanar katse duk wani tallafin kasashen turai.

Yanzu haka dai kasashen Faransa, Jamus, da kuma Biritaniya, na shirin fitar da wata sanarwa ta bai daya, ta yi tir da kakkausar murya kan matakin na Turkiyya.

A nata bangare kuwa majalisar dokokin AMurka, ta ce shugaban kasar ta Turkiyya Recep Tayyip Erdogan, zai dandana kudarsa akan wannan matakin da ya dauka, kan kurdawa kamar yadda dan majalisa repablicain,Lindsey Graham, ya sanar.

Post a Comment

0 Comments

Close Menu