Shugaban majalisar dokokin Iran ya ce kafin fara yakin kasashen siriya da Yemen sun bayar da shawarar tattaunawa, amma wasu kasashe suka dage kan yaki, kuma yanzu ya tabbata cewa rikicin kasar Siriya ba za a iya magance shi ta hanyar amfani da karif soja ba.

Kamfanin dillancin labaran Irna ya nakalto shugaban Majalisar dokokin kasar Iran Ali Larijani a gefen taron kungiyar majalisu na Duniya wato IPU dake gudana a birnin Belgrade fadar milkin kasar Serbia na ganawa da Souleymane Shainain shugaban majalisar dokokin kasar Aljeriya inda ya bayana mahimancin alaka da kuma hadin kai tsakanin kasashen musulinci.

Larijani ya ce kafin fara yakin kasashen siriya da Yemen sun bayar da shawarar tattaunawa, amma wasu kasashe suka dage kan yaki, kuma yanzu ya tabbata cewa rikicin kasar Siriya ba za a iya magance shi ta hanyar amfani da karif soja ba.

Har ila yau Larijani ya bayyana al'ummar kasar Aljeriya da al'umma mai basira don haka cikin kankana lokaci za su magance matsalar cikin gida da kasar ke fama da shi.

A bangare guda kuma Dakata Ali Larijani ya gana da Ahmad Ali Mahmud shugaban Majalisar dokokin kasar Qatar.