Ministan harakokin wajen Rasha Sergey Lavrov ya tabbatar da cewa kasar Rasha dake a matsayin kasa ta biyu dake sayar da makamai a Duniya za ta ci gaba da zartar da yarjejeniyar da ta kula da hukumomin iraki na sayarwa kasar makamai.

A yayin da ya kai ziyara kasar Iraki a wannan litinin, ministan harakokin wajen kasar Rasha Sergey Lavrov ya gana da takwaransa na kasar Iraki inda suka bayana wajibcin ci gaba da zartar da yajejeniyar kasuwanci da tattalin arzikin da suka kula a watan Afirilun da ya gabata, daga cikin wannan yarjejeniya harda sayarwa kasar ta Iraki makaman yaki.

A nasa bangare, ministan harakokin wajen kasar Iraki Muhamad Ali Al-Hakim ya ce lokaci yayi da za su karfafa alakar kasuwanci tsakanin biranan Bagdaza da Moscow, musaman ma karfafa aiki tare a bangaren makamashi da tsaro da man fetir gami da iskar gaz.

A wannan Litinin ne Ministan harakokin wajen kasar Rasha Sergey Lavrov ya fara ziyarar aiki a birnin Bagdaza fadar mikin kasar Iraki