Gwamnatin hadin kan kasar Libiya ta bukaci kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya da ya sanya sunan khalifa haftar cikin jerin sunayen da kwamitin ya kakabawa takunkumi.

Kamfanin dillancin labaran Tasnim ya habarta cewa a jiya laraba, ma'aikatar harakokin wajen gwamnatin hadin kan kasar Libiya dake birnin Tripoli ta aike da wasika zuwa ga shugaban kwamitin tsaron MDD, inda ta bukaci ya sanya sunan janar khalifa Haftar cikin jerin sunayen da kwamitin ya kakabawa takunkumi domin ya fuskanci hukunci.

Wasikar ta ce hare-hare kan fararen hula wadanda ba su ji ba su gani ba, da kuma gidajen fararen hula ya karya hakin-adama, don haka bisa doka mai lamba 22 kudiri na 1970 wacce aka samar a shekarar 2011, da kuma kudiri mai lamba 2174 da aka samar a shekarar 2014, ya zamanto wajibi a sanya suna khalfi haftar cikin wanda kwamitin ya kakabawa takunkumi kuma ya fuskanci hukunci daga kwamitin.

Har ila cikin wasikar, an bayaana cewa dakarun Haftar na ci gaba da kai hare-hare kan gidajen fararen huka a birnin Tripoli da kewayensa, da kuma mahiman wurare kamar filayen sauka da tashi na jiragen saman gariruwan Tripoli da Misratah.

Alkaluma sun ce daga lokacin da jahar Khaftar ya kaddamar da wannan hari zuwa yanzu kimanin mutane 510 ne suka rasa rayukansu yayin da wasu sama da 2000 na daban suka jikkata