Kamfanin dillancin labarun Anatoli na kasar Trukiya ya Ambato ma’aikatar tsaron kasar tana bayyana cewa; Farmakin da suke kai wa a cikin kasar Syria yana samun nasara.

A yau Litinin harin da Turkiya take kai wa a kasar ta Syria ya shiga cikin kwanaki na shida, wanda kamar yadda mahukuntan kasar suka bayyana, yana nufin kawo karshen barazanar Kurdawa.
Sai dai kasashe da dama da kungiyoyin kasa da kasa da suka hada da MDD sun bayyana harin na Turkiya da cewa ya sabawa doka, kuma keta hurumin wata kasa ce mai ‘yanci.

Jamhuriyar Musulunci ta Iran,ta bakin ministanta na harkokin waje Muhammad Jawad Zarif ya fadawa tashar talabijin din Turkiya ta TRT cewa; Ba a samun tsaro ta hanyar kai wa wata kasa hari.