Madugun ‘yan tawayen Sudan ta Kudu, kana tsohon mataimakin shugaban kasar, Riek Machar, ya isa Juba babban birnin kasar, a wani yunkuri na neman ceto yarjejeniyar zaman lafiya da aka cimma don kafa gwamnatin hadin kan kasa da shugaba Salva Kiir.

Tun da farko dai an tsara yadda bangarorin biyu zasu gana cikin sirri a fadar shugaban kasar, kamar yadda kakakin jam’iyyar SPLM-IO, ta Riek Mashar ya sanar.

Bayanai dai sun ce yarjejeniyar zaman lafiyar da aka cimma a watan Satumba na 2018, ta taimaka sosai wajen samun dan sukuni a wannan kasar ta Sudan ta Kudu da yaki da daidaita.

Ranar 12 ga watan Nuwamba mai zuwa ne aka kayyade za’a kafa gwamnatin hadin kan kasar, inda madugun ‘yan tawayen, Riek Mashar, zai sake karbar tsohon mukaminsa na mataimakin shugaban kasa.

Kasar Sudan ta Kudu, ta dai fada cikin yakin basasa ne a watan Disamba na shekara 2013, shekaru biyu bayan data samu ‘yanci kai, lokacin da Mista Kirr, dan kabilar Dinka, ya zargi mataimakin nasa M. Machar, dan kabilar Nuer, da shirya masa juyin mulki.

Mutane sama da dubu dari uku ne suka rasa rayukansu, a rikicin kasar, tare da cilastawa sama da miliyan hudu tserewa daga gidajensu.