Mahukuntan kasar Saudiyya sun aike da sakonnin wasiku zuwa ga shugaban kasar Iran Hassan Rauhani.

A lokacin da yake zantawa da manema labarai jiya a birnin Tehran, kakakin gwamnatin Iran Ali Rabie ya tabbatar da cewa gwamnatin Saudiyya ta aike da wasu awasu zuwa ga shugaban kasar Iran a cikin ‘yan lokutan da suka gabata.

Rabie ya bayyana hakan ne a lokacin da aka tambaye shi danagane da gaskiyar bayanan da ke cewa, mahukuntan na Saudiyya suna neman taimakon Iran wajen shawo kan yakin da suke yi a Yemen, wanda a halin yanzu mayakan na Yemen suke mayar da mummunan martani kan kasar ta Saudiyya.

A akan wanann batu Rabie ya bayyana cewa, hakika mahukuntan Saudiyya sun aike da sakonni na wasiku zuwa ga shugaba Rauhani, amma bai yi Karin haske kan abin da wasikun suka kunsa ba, amma dai ya bayyana cewa abin da yake mafita wanda kuma zai kawo karshen wannan matsala, shi ne Saudiyya ta kawo karshen hare-harentakan al’ummar kasar Yemen.