Majalisar dinkin duniya ta yi maraba da sakin fursinonin yaki wanda gwamnatin kasar Yeman ta yi, sannan ta bayyana hakan a matsayin abban mataki na shirin musayar fursinoni tsakanin kasar da kuma kasashen da suke fafatawa da ita.

Tashar talabijin ta Al-Alam a nan Tehran ta nakalto jakadan majalisar dinkin duniya na musamman kan yakin da ake yi a kasar Yeman Mr Martin Grafiy yana fadar haka a shafinsa na tweeter a jiya litinin.

Grafit ya yaba da matakin da kwamitin fursinonin yaki na kasar yemen ta dauka na sakin fursinonin yaki 350 daga ciki hard a yan kasar saudia biyu.

Kafin haka dai Abdul kadira Murtadha shugaban kwamitin fursinonin yaki a kasar Yemen ya bada sanarwan sakin fursinoni 350 a jiya litinin , sannan ya ce tuni ya mikawa hukumomin majalisar dinkin duniya jerin sunayen fursinonin da kwamitin ya sallama, kuma ya mikasu ga MDD a jiya litinin, sai kuma yana fatar dayan bangaren ma zai yi haka.