Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

*Majalisar Dinkin Duniya Tana Fuskantar Karancin Kudade*
Babban magatakardar MDD Antonio Guterres ne ya bayyana cewa; matsalar karancin kudaden da suke fuskanta shi ne mafi muniacikin shekaru 10 na bayan nan.

A Jiya Talata ne dai babban magatakardar Majalisar Dinkin Duniyar ya fadawa kasashe mambobi cewa; MDD tana fuskantar barazanar fitar samun koma bayan kudadenta, da kuma gajiyawa wajen biyan kudaden ma’aikatanta a karshen wannan watan.

Guterres ya kara cewa; Ya zuwa yanzu an bayar da kaso 70% na jumillar kudaden da MDD take bukatuwa da su a 2019, wanda shi ne dalar Amurka biliyan 1.99.

Gutress ya kara da cewa; Matukar kasashe ba su biyu kudadensu na shekara-shekara ba, to muna fuskantar barazana wajen tafiyar da ayyukanmu da kuma sauye-sauyen da muke son aiwatarwa.

Post a Comment

0 Comments

Close Menu