Majalisar gwamnoni a tarayyar Najerita ko NGF ta bayyana cewa yerjejeniyar mafi karancin albashi tsakanin gwamnatin tarayyar da kuma kungiyoyin kwadago na ma’aikatan tarayyar ne kawai, bai zama wajibi a kan jihohi su aiwatar da ita ba.

Jaridar Premim times a Najeriya ta nakalto shugaban majalisar gwamnonin, koma gwamnan jihar Ekiti Kayode Fayemi yana fadar haka a jiya Litinin a Abuja.

Fayemi ya kara da cewa yerjejeniyar da kungiyoyin kwadago suka cimma da gwamnatin tarayyar a ranar 18 ga watan Octoba da muke cike ta shafi ma’aikatan gwamnatin tarayyar ne, kuma ko gwamnatin tarayyar ta amince da yerjejeniyar ne don kaucewa barazanar yajin aikin ma’aikata ne.

Shugaban majalisar gwamnonin ya kara da c ewa jihohi suna da kungiyoyinsu na gwadago a jihohinsu, sannan suna da majalisun dokokin wadanda su ne suke yanke shawara kan dukkan lamuran a jihohinsu.

A ranar laraban da ta gabace ce majalisar ministoci karkashin shugabancin mataimakin shugaban kasa ta amince da albashi mafi karanci na naira dubu 30 ga ma’aikata, kuma ta amince a fara biyan sa daga ranar 18 ga watan Octoban da muke ciki, sai kuma basussukan da ma’aikata suke binta za’a biya kafin karshen shekara.