Shugabar majalisar wakilan Amurka Nancy Pelosi ta bada sanarwan cewa majalisar wakilan kasar zata gudanar dazama na musamman don bayyana ra’ayinta kan batun tsige shugaban kasar ta Amurka Donal Trump daga kan mukaminsa.

Tashar talabijin ta CNN ta nakalto Pelosi tana fadar haka a ranar Litinin da ya gabata, ta kuma kara da cewa, a bisa tsaron doka zaman ba wajibi bane, amma kuma majalisar tana da damar tsige shugaban kasa ko wani mai babban mukami a kasar.

Banda haka Nancy Pelosi ta kara da cewa a ranar Alhamis mai zuwa ce za’a gudanar da zaman, inda ya majalisar zasu tabbatar ko su yi watsi da zancen cewa shugaban shugaba Trump ya yi shishigi a cikin binciken da ake masa kan wasu laifuffukan da ake tuhumarsa da aikawa.

Idan ta amince, daga nan ce za’a fara tattauna batun tsige shi din.

Tace ya zuwa yanzu dai suna da shaidu kan cewa shugaban ya hana wasu dakardun shaidan da majalisar ta bukace shi ya bada su, sannan ya hana wasu shaidu zuwa majalisar don bada shaida a kansa.

Da sauransu.