Kamfanin dillancin labaran AFP na kasar Faransa ya nakalto sakataren tsaron kasar Amurka Mark Esper yana fadar cewa za a dauki makonni ana aiwatar da shirin janyewar sojojin Amurka kimanin dubu guda daga kasar ta Siriya zuwa Iraki, kuma ana amfani da jiragen sama da kuma motoci don aiwatar da shirin.

Esper ya kara da cewa idan an kammala aikin janyewar jimillar sojojin Amurka a kasar Iraqi zai kai 6000, kuma babban aikinsu shi ne kare kasar ta Iraqi da kuma ci gaba da yakar kungiyar Daesh.

A wani rahoton kuma har’ila yau biyo bayan janyewar sojojin Amurka daga kasar ta Siriya ita ma gwamnatin kasar Britaniya ta bada sanarwar janyewar sojojinta daga kasar da gaggawa zuwa yammacin kasar Iraqi.
‘Yan siyasa da dama a kasar Amurka suna sukar shugaban Trump dangane da janyewar sojojin kasar daga kasar Siriya, saboda barin kungiyar kurdawa ta Syrian Kurdish Democratic Union Party (PYD) wadda take kawance da Amurka a hannun sojojin Siriya ko kuma sojojin kasar Turkiyya.