Gwamnatin Malawi da bangaren ‘yan adawa na kasar da kawancen masu rajin kare hakkin dan Adam HRDC, sun ce sun shirya tsaf domin hawa teburin sulhu don kawo karshen rikicin kasar da ya biyo bayan sanar da sakamakon zaben shugaban kasar da aka yi a ranar 21 ga watan Mayu.

Wannan na zuwa ne mako guda, bayan da MDD da ofisoshin jakadanci 6 dake Malawi, suka yi tir da rikicin bayan zaben kasar, suna masu kira da a gaggauta hawa teburin sulhu tsakanin gwamnatin ta Malawi da dukkan masu ruwa da tsaki, domin kawo karshen rikicin siyasar kasar.

Kawo ya zuwa yanzu, rikicin bayan zaben ya yi sanadin mutuwar mutane 4 da lalata kadarorin da darajarsu ta kai miliyoyin daloli.

Gwamnatin Malawi da 'yan adawa da kungiyar HRDC, sun shaidawa kafafen yada labaru na kasar cewa, sun shirya tattaunawa da nufin kawo karshen rikicin kasar kafin ya yi Kamari.