Wasu ‘yan bindiga da ake kyautata zaton cewar masu riya jihadi ne, sun sace malamai 6 a yankin tsakiya Mali, saboda koyar da harshen faransaci da kuma magana da ita.

Jaridar Leadership ta Hausa ta nakalto wani shaidar ganin ido, wanda ya ce kafin a sace malaman, sai da ‘yan bindigar suka kona tarin litattafan dalibai a farfajiyar makarantar. Harin na baya bayan nan dai ya zo ne bayan da wata kididdiga ta nuna cewar, sama da makarantu 900 ne aka rufe a sassa daban-daban na kasar ta Mali, sama kashi 2 bisa 3 daga cikin makarantun suna yankin tsakiyar kasar, saboda yawaitan matsalolin tsaro a yankin wadanda suka hada ayyukan ta’addanci da kuma rikicin kabilanci.

A shekarar 2012 matsalar tsaro ta kunno kai a Mali, bayan da mayaka masu riya jihadi da suka yi wa kungiyar Al-Qaeda mubaya’a suka mamaye arewacin kasar, bayan da sojojin kasar suka gaza murkushe tawayen Azbinawa.

Sai dai a shekarar 2013 dakarun Faransa suka kawo dauki, inda suka yi nasarar kwace mafi yawan yankunan da mayakan suka mamaye.