Tashar al’alam ta bayar da rahoton cewa, gwamnatocin duniya daban-daban sun bayyana matsayarsu dangane da sanarwar da shugaban Amurka Donald Trump ya bayar dangane da kisan Baghdadi, inda kasashen turai da dama suka bayyana hakan da cewa babban ci gaba ne a fagen yaki da ta’addanci.

A nata bangaren gwamnatin kasar Rasha ta bayyana cewa, ba ta da wasu dalilai da suke tabbatar da gaskiyar abin da Amurka ta fada dangane da kisan Baghdadi, amma indan har hakan da gaske ne, bay a nufin kawo karshen ISIS ba ne.

Ita ma a nata bangaren gwamnatin Iran ta bayyana kisan Baghdadi da cewa, ba zai kawo wani babban sauyi dangane da barazanar da ta’addanci ke yi wa al’ummomin duniya ba, domin wadanda suka samar da Abubakar al-baghdadi kuma suka dauki nauyinsa suka ba shi kariya tsawon shekaru, su ne kuma suka sanar da kashe a yanzu.

Da dama daga cikin masana siyasar duniya kuma suna bayyana kisan na Baghdadiahalin yanzu da cewa yana da alaka da batun siyasa, musamman ganin cewa zabuka na karatowa a kasar ta Amurka.