Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

Masar Da Habasha Zasu Gana A Rusha kan Madatsar Ruwan Annahdah


Shugaban kasar Masar Abdulfatta Assisi ya bayyana cewa zai gana da Firai ministan kasar Habasha Abir ahmed a birnin musko a karshen wannan watan inda yake saran zasu tattauna batun madatsar ruwa ta Annahdah wanda ake ginawa a kan kogin nilu a kasar Habasha a halin yanzu.

Kamfanin dillancin labaran reuters ya nakalto shugaban yana fadar haka a jiya Lahadi, a birnin Alkahira inda ya bayyana damuwar gwamnatinsa dangane madastar ruwan, wanda yake ganin idan an kammala gina ta hakan zai iya jawo karancin ruwa mai tsanani a kasar Masar.

Kamfanin dillancin labaran reuters y ace shugaban bai bayyana lokacin haduwarsa ta Ahmed a kasar ta Rasha, amma akwai taron Rasha da kasashen Afrika wanda za’a gudanar a birnin Sochi nab akin ruwan tekun Black sea a ranakun 23-24 ga watan Octoba da muke ciki.

Post a Comment

0 Comments

Close Menu