Wasu gungun mata musulmi sun gudanar da jerin gwano na lumana a birane daban-daban na kasar Ghana, domin nuna rashina mincewa da yadda ake nuna musu wariya saboda saka hijabin musulunci.

Jerin gwanon ya gudana ne a birane daban-daban musamman ma Accra babban birnin kasar, da kuma biranen Tamale da Kumasi, inda mata musulmi masu yawa suka fito domin nuna korafinsu.

Da dama daga cikin mata musulmi akasar ta Gahana suna kokawa ne kan irin wariyar da ake nuna musu saboda saka hijabin muslunci, musammana a lokutan da suke neman aiki, inda akan ki daukarsu idan an gan su sanye da hijabi.

Masu jerin gwanon sun yi ta rera taken da ke tabbatar musu da hakkinsu na saka hijabi a matsayinsu na musulmi, inda suke bayyana hakan a matsayin akidarsu ta musulunci, wanda kundin tsarin mulkin kasar ta Ghana ya yarje musu da hakan.