Babban sakatare na MDD, Antonio Guteress ya ce ya damu matuka da yadda ake fuskantar jerin zanga zanga nan da cen a kasashen duniya, inda har ma a wasu lokutan ake samun hasara rayuka na mutane.

Mista Guteress ya danganta lamarin da babban gibin da ake fuskanta tsakanin jama'a da kuma ‘yan siyasa.

A don hana ne babban sakataren na MDD ya bukaci shuwagabannin kasashen duniya dasu samar da siyasa ta gari domin kyatatawa jama’arsu.

Mista Guteress yayi ammanar cewa zanga zangar da ake fuskanta a nahiyoyi daban daban na duniya, suna da alkibla gula ce, wacce ita ce rashin yarda da ya bullo tsakanin jama’a da kuma magabata.

Saidai a hannu guda kuma Mista Guteress, ya nemi masu zanga zangar dasu kai zuciya nesa, su dauki misali da irin gwagwarmayar da su Martin Luther King da kuma Gandhi sukayi, sannan kuma su ma jami’an tsaro su bar amfani da karfi wajen murkushe masu zanga zangar.

A baya bayan nan dai ana fuskantar jerin zanga zanga a kasashen da suka hada da Chili, Iraki da Labanon da Kazakstan da kuam Guinea.