Sakatare Janar na MDD Antonio Guterres, ya yi kira ga kasashen Afrika su magance matsalolin ta'addanci da sauyin yanayi domin wanzar da tsaro da zaman lafiya.
Yayin wata muhawara ta Kwamitin Sulhu na MDD kan matakan diflomasiyya da na kare rikici da yin sulhu a Afrika, Antonio Guterres ya ce ta'addanci barazana ce dake karuwa a fadin nahiyar Afrika, wanda kuma ke mummunan tasiri kan zaman lafiya da tsaro.

Ya ce a yankin Sahel, kungiyoyin 'yan ta'adda kan kai hare-hare kan dakarun yankin har ma da na kasa da kasa, sannan rikici na bazuwa a kasashen dake kan gabar tekun Guinea.

Ya ce a Nijeriya kuwa, Boko haram da rassanta, sun addabi al'ummomin, tare da farwa jami'an tsaro, duk da kokarin sojojin kawancen kasashe.

Antonio Guterres ya nemi tallafin ayyukan soji, ciki har da shirin wanzar da zaman lafiya na Tarayyar Afrika dake aiki a Somalia da dakarun kawancen kasashen yankin Sahel 5 da kuma dakarun kawance na kasashen wajen yaki da Boko Haram.

Har ila yau, ya ce magance sauyin yanayi, matakin kariya ne mai muhimmanci, domin matsalolin yanayi da suka hada da fari da ambaliya da sauyin yanayin saukar ruwar sama, wanda ke da alaka da batutuwan siyasa da zamantakewa da tattalin arziki, wanda ke bukatar tallafawa kasashen da matsalar ta fi shafa.