Kwamitin tsaro na MDD, ya amince tsawaitawa da gagarimin rinjaye matakin binciken jiragen ruwan da ake shakku akansu kan safara bakin haure a gabar ruwan Libiya.

A zamansa na ranar Alhamis, data gabata kwamitin, ya tsawaita da shekara guda matakin dake baiwa rundinar tarayyar turai ta Sophia gudanar da aikin binciken a tekun mediteranien.

Matakin dai na zuwa ne a daidai lokacin da kasashen dake cikin rundinar ta Sophia, basa da jiragen ruwa a yankunan da matsalar ta shafa domin tabbatar da aikinta, saboda matakin kasar Italiya, na hana sabke bakin hauren da aka kwaso daga teku a tashoshin ruwan ta.

Kwamitin tsaron na MDD, ya kuma yi tir da duk wani salo na safara bakin haure daga Libiya ko azabtar dasu.