Cibiyar kula da taron arbaeen a Karbala ta sanar da cewa maukibi dubu 10 da 700 ne za su halarci taron arbaeen.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Rayyad Ni’imah Alsalman mai kula da tawagogin maukibi a tarukan arbaeen ya bayyana cewa a bana maukibi dubu 10 da 700 ne za su halarci taron arbaeen na wannan shekara.

Ya ci gaba da cewa dukkanin wadannan maukibobi sun aiko da sunayensu da kuma tsare-tsarensu da adadin mutanensu, kuma za su zo ne daga kasashe 21 na duniya.

Haka nan kuma ya yi ishara da cewa, akwai dubban mutane daga cikin maukibobin wadanda aikinsu shi ne yin hidima ga masu ziyarar.

Dangane da tsare-tsaren da suke da su ya ce, masu hidima a hubbaren Imam Hussain (AS) da kuma hubbaren Abbas (AS) ne za su dauki nauyin kula da dukkanin masu ziyarar a hubbarorin biyu, tare da taimakon wasu masu sa kai daga sassa na kasar ta Iraki.