Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

Ministan Tsaron Yemen Ya Gargadi 'Yan Koran Saudiya


Ministan tsaron gwamnatin ceton al'ummar Yemen ya ja kunan 'yan korar Saudiya, matukar dai ba su fice daga cikin kasar ba, to za su fuskanci farmaki daga bangaren Sojin kasar

Cikin wani bayani da ya fitar a jiya Litinin, Ministan tsaron kasar Yemen Muhamad Nasir Atify ya ce hadin kai shi ne tushe samun nasara da dakarun kasar suka yi a yakin da suke yi da 'yan mamaya.

Atify ya gargadi sojojin hayar saudiya 'yan kasar Sudan da su fice daga cikin kasar cikin gaggawa, idan kuma ba haka, to su kasance cikin ko ta kwana domin za su fuskanci babban farmaki daga dakarun tsaron kasar ta Yemen.

Wannan jan kune na Ministan tsaron yemen din na zuwa bayan wani farmaki da Sojojin kasar suka kai kan dakarun kasar Saudiya da 'yan korarsu a ranar Asabar din da ta gabata, inda suka kashe akalla Sojoji 500 da kuma kame wasu kimanin dubu biyu na daban.

A bangare guda kuma gwamnatin kasar ta Yemen ta saki fursunonin yaki 290 a wani mataki na yarjejeniyar sulhu da aka cimma a shekarar bara.

Tuni dai manyan kungiyoyin agaji na kasa da kasa suka yi maraba da matakin na Huthi inda kungiyar Red Cross ta ce yunkuri ne dai zai kawo nasara a kokarin da ake na sasanta rikicin kasar ta Yemen.

Post a Comment

0 Comments

Close Menu