Babbar jami'a mai kula da harkokin siyasar wajen kungiyar tarayyar turai Federica Mogherini ta kirayi Turkiya da ta kawo karshen hare-haren da ta ke kaddamarwa a kan yankunan arewacin Syria.

Jaridar El Pais ta kasar Spain ta bayar da rahoton cewa, a jiya Jum'a Federica Mogherini ta kirayi Turkiya da ta kawo karshen hare-haren da ta ke kaddamarwa a kan yankunan arewacin Syria ba tare da wani bata lokaci ba.

Mogherini ta bayyana harin na Turkiya a kan yankunan Kurdawan Syria da ke arewacin kasar da cewa ba ya kan ka'ida, kuma hakan ya saba wa dukkanin dokoki na kasa da kasa.

A ranar Alhamis da ta gabata ma majalisar kungyar tarayyar turai ta fitar da wani bayani da ke yin tir da hare-haren na Turkiya a kasar Syria.

Gwamnatin Turkiya ta fara kaddamar da hare-haren ne a kan yankunan Kurdawan Syria da ke kan iyaka da kasar, inda take bayyana su da 'yan ta'adda.