*

Kakakin ma'aikatar harakokin wajen kasar Iran ya bayyana shirin kasarsa na shiga mataki na hudu na jingine wani bangaren yarjejeniyar nukiliyar da kasar ta cimma tare da manyan kasashen Duniya a shekarar 2015.

Cikin wani taron manema labarai da ya gabatar a wannan Litinin, kakakin ma'aikatar harakokin wajen jamhoriyar musulinci ta Iran sayyid Abbas Mousavi ya bayyana cewa kasar na shirin shiga mataki na hudu na jingine wani bangare na yarjejeniyar nukiliyar da kasar ta cimma tare da kasashen Duniya.

Mousavi ya bayyana cewa matukar dai kasashen da suka rage cikin yarjejeniyar ba su cika alkawarin da suka dauka ba, to kasar za ta shiga mataki na hudu na jingine wani bangare na yarjejeniyar.

Yayin da aka tambaye shi kan shirin kasashen Faransa da japon na baiwa kasar bashin dala biliyan 18 domin kiyaye yarjejeniyar nukiliyar ya ce wannan shiri ne da kasar Faransa ta bayar a baya amma babu inda aka je kan batun, ganin cewa sai wata kasa ta bayar izini, don haka babu wani sakamako.

Yayin da yake ishara kan rikicin baya-bayan nan na kasar Labnon, Mousavi ya ce kasar Iran ba ta yin katsa landan kan harakokin wata kasa, to saidai muna fatan kungiyoyi da jam'iyun siyasa za su tattaunawa domin fitar da kasar daga rikicin da take ciki a yau.

Dangane da kokarin da kasar Turkiya ke yi na kafa sansanin Soja a kasar Siriya.

Mousavi ya ce hukumomin Turkiya nada damar kafa sansanin soja a kan iyakokinsu, amma a cikin wata hakan ya sabawa dokokin kasa da kasa.