Babbar jam’iyyar adawa ta Renamo a Mozambique, ta yi watsi da sakamakon manyan zabukan kasar da aka gudanar a ranar 15 ga watan Oktoba, tare da kiran a sake zabukan.

Jam’iyyar ta Renamo ta kuma bukaci ‘yan kasar da su yi watsi da sakamakon zabukan, wadanda ta ce an gudanar da su cikin kura-kurai masu yawa.

Dama kafin hakan masu sanya ido na kasa da kasa a zabukan sun nuna damuwarsu akan kura- kuran da suka ce an tafke nan da can a zabukan.

Sakamakon wucin gadin da hukumar zaben kasar ta fara fitarwa a ranar Juma’ar da ta gabata, ya yi nuni da cewa jam’iyya Frelimo mai mulki ce ta shugaban kasar Filipe Nyusi, ke kan gaba, da babbar tazara a sakamakon.

A nata bangare jam’iyyar ta Frelimo ta wallafa da yammacin jiya a shafinta na intanet cewa shugaban kasar ne Nyusi ke kan gaba da kashi 74% a yayin da babban abokin hamayarsa Ossufo Momade ke da kashi 20 cikn dari a sakamakon mazabu biyu cikin uku.