WAMUSIBATA 

INNA LILLAHI WA INNA ILAIHIR RAJI'UN


ANNABI MUHAMMAD(SAW) YA YI SHAHADA (WAFATI) A RANAR 28 SAFAR, SHEKARA TA 11 H:

Ranar Litinin, 28 ga watan  Safar; ita ce ranar da fiyayen halita; Annabi Muhammad(saw) yayi shahada!

Ranar ce ta fi ko wace rana duhu!

Ranar ce ta fi kowa ce rana zama ranar bakin-ciki!

Ranar da inuwa ta gushe!

Ranar da tsaraici ya bude!

Ranar da duk Halitu suka yi kuka!

Ranar da Mala'iku(as) suka yi bakin-ciki!

Ranar da Al-arshi ya girgiza!

Ranar da Sama ta yi kuka!

Ranar sa kasa ta shiga Damuwa!

Ranar Da Shugabar Matan Duniya da Lahira ta yi kuka!

Ranar da mai rabon Al-jannah ya shiga damuwa!

Ranar da shuwagabanin Samarin Al-jannah suka zama marayu!

Ranar da Zainabul-kubra(as) ta ga kyara!

Ranar da Sayada Nana Zakiya(as) ta ke kuka, tana cewa; na rasa gatana!

Wa Musibatahu!

Wa Waila!

Wa Muhammad(saw)!

Wa Ahmad(saw)!

Wa Rasulullah(saw)!

Bayan Hajjin bankwana da cikar addini; sai Annabi Muhammad(saw) ya yi rashin lafiya mai sauki, saboda gubar da aka saka masa, sai dai rashin lafiyar ya yi tsanani har sai da ya hadu da Ubangijinsa a 28 ga watan safar na 11 H.

Imam Ali(as) ne ya yi masa wanka, sallah da binne shi a dakinsa a Madina, inda kabarinsa yake yanzu; tare da taimakon wasu Sahabbai.

Annabi Muhammad(saw) ya kansace abin koyi a rikon amana, ikhlasi; gaskiya, cika alkawari, kyawawan halaye, girma, kyawawan dabi'u, baiwa, ilmi; hakuri, rangawame; afuwa, sadaukantaka, tsentseni, takawa, zuhudu, baiwa, adalci, kaskan da kai, jihadi da sauran dukkan nagarta da halaye nagari.

Jikinsa ya kasance kololuwa wajen kyau da kuma daidaito, fuskarsa kamar wata ne mai haske da ya cika, zuciyarsa da ruhinsa sun kai matuka wajen kamala, mafi kamalar halaye da ladabi da dabi'a kuma sunnarsa ta hakika tana haske kamar rana a tsaka-tsakinta.

Annabi Muhammad(saw) shine Annabin karshe, ya tattara dukkan dabi'u masu kyau: girma, daukaka, ilimi, adalci, takawa da kuma iya tafiyar da al'amuran duniya da na lahira, wadanda babu wani mahaluki da yake da irin kyawawan dabi'unsa.

➖➖➖➖➖➖➖➖
KNPRSCD 04
KADUNA PRESS
BASHEER MUHAMMAD

🌹🌈🌹🌈🌹🌈🌹🌈🌹