Kakakin ma'aikatar harakokin wajen kasar Iran ya nuna damuwarsa da abin da ke faruwa a kasar Iraki wanda ya yi sanadiyar salwantar rayukan mutane da dama da kuma jikata wasu na daban da kuma lalata dukiyoyin al'umma, inda ya ce Iran na sa ido kan abubuwan da ke faruwa a kasar ta Iraki.

Cikin wata sanarwa da ya fitar a daren jiya Asabar, kakakin ma'aikatar harakokin wajen jamhoriyar musulinci ta Iran Sayyid Abas Musavi ya ce Iran na goyon bayan bukatun al'ummar kasar Iraki da kuma bayanan da malaman addini da kuma firaministan kasar suka fitar.

A bangare guda kuma, Musavi ya nuna tsananin damuwarsa kan abubuwan baya-bayan nan da suka faru a kasar ta Iraki wanda ya yi sanadiyar mutuwa da kuma jikkatar mutane da dama tare da barnata dukiyar gwamnati da fararen hula.

Sayyid Abas Musavi ya tabbatar da cewa daga lokacin da aka kafa sabuwar gwamnatin Iraki, jamhoriyar musulinci ta Iran ta ci gaba da goyon bayan gwamnati da al'ummar kasar, kuma a lokacin matsala, iran din na tare da al'ummar Iraki har zuwa lokacin da za a magance matsalar.