Rahotanni daga Iraki na cewa mutane 60 ne suka rasa rayukansu da suka hada da 18 a Bagadaza, tun bayan barkewar zanga zanga a kasar a ranar Talata data gabata.

Wasu alkalumma daga majiyoyin gwamnati da kamfanin dilancin labaren AFP, ya fitar sun kuma nuna cewa akwai daruruwan mutane da suka samu raunuka.

A ranar Talata data gabata ce aka fara zanga zangar data samo asali daga shafukan sada zumunta, akan cin hanci da rashawa da rashin aiki.

Rahotanni daga kasar sun ce ko a jiya Juma’a ma an sha artabu tsakanin jami’an tsaro da masu zanga zangar, duk da dokar ta bacin da aka kafa, da kuam katse hanyoyin sadarwa na intanet.