An rufe babban shagon kasuwanci na zamani dake Manchester din,inda nan ne aka kai harin.

Kafafen watsa labarun Birtaniya sun ce; Ana yi wa mutane hudu da su ka sami raunuka magani bayan harin na shagon Arndale.

Jami’in ‘yan sandan da suke fada da ayyukan ta’addanci y ace; Mutane biyar ne aka sara da wukar, kuma tuni sun fara gudanar da bincike akan lamarin