Mutanen yankin arewa maso gabacin kasar Siriya kimani dubu 100 suka yo gudun hijira daga yankunansu bayan da gwamnatin kasar Turkiya ta kaddamar da yaki a kan yankin a ranar laraban da ta gabata.

Labarin ya kara da cewa mayakan kungiyar yan ta’adda ta Daesh 5 suka tsere daga kurkukun Jirkin na garin Qamishlia arewa maso gabacin kasar ta Siriya bayanda sojojin Turkiya suka fara kai farmaki a kan yankin.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta ce dukkan masu gadin gidajen yari a yankin sun gudu, sannan ta nakalto shugaban kunngiyar Kurdawa ta “Syrian Democratic Forces” (SDF) wacce take iko da yankin, Mustafa Bali, yana cewa, daga yanzun kuma mayakan kungiyar Daesh kimanu 12,000 da suke tsare sun fice daga ikonsu, hakama iyalan mayakan na Daesh kimani dubu 90,000 wadanda aka tsugunar da su a wani sansani a yankin su ma ba sa karshen ikon kungiyar daga yanzu.

Mustafa Bali, ya kara da cewa a halin yanzu gwamnatin kasar Turkiyya ta kaddamar da yaki a kansu, don haka ba su da zabi in banda kare kansu daga mamayar sojojin Turkiyya.