Hukumar Zaben kasar Ajeriya ta sanar da cewa ya zuwa yanzu mutane 22 ne su ka yi rijsitar son yin takarar shugabancin kasar wanda za a yi a cikin watan Disamba na wannan shekarar.

Daga cikin wadanda su ka mika takardunsu na son tsayawa takarar shugabancin kasar ta Aljeriya wanda shi ne karo na farko bayan shugaba Abdulaziz Butefkila, da akwai Ali Benflis wanda tsohon Fira minista ne da kuma AbdulMajid Tebboune.
An tsaida ranar 12 ga watan Disamba ne a matsayin ranar karshe mika takardunsu na son tsayawa takarar shugabancin kasar ta Aljeriya.

Al'ummar kasar Aljeriya suna yin Zanga-zanga domin hana duk wanda ya taba rike mukami a gwmanatin Butefkila sake tsaywa takara ko rike wani mukami.