Masu sharhi a Najeriya sun ce halin tabarbarewar tsaro na kara sanya fargaba a zukatan 'yan kasar, duk da cewa hukumomi suna cewa matsalar ba ta kai yadda ake zuzutawa ba.
Ko a yammacin ranar Lahadi 'yan sanda sun ce sun kubutar da wani babban jami'insu daga hannun masu satar mutane don neman kudin fansa a hanyar Kaduna zuwa Jos.
Malam Kabiru Adamu wani kwararre ne kan harkokin tsaro a Najeriya, ya shaida wa BBC cewa daga watan Janairun 2019 zuwa yanzu an sace mutum 700 a fadin kasar.
"Bisa ga alkaluman da muke da su, a bana kawai an sace dan adam dai-dai har misalin 700 a fadin kasar. Wadannan alkaluma ba wai dole ba ne abin ya zama haka yake amma gwaji ne wanda zai nuna wa duk mai bibiyar lamarin inda matsalar take," in ji shi.