Kamar yadda a ka saba a duk shekara, 'yan'uwa Musulmi almajiran Shaikh Ibraheem Zakzaky sun gudanar da Tattakin Arba'in na Imam Husaini a domin  tunawa da kwanaki 40 da kisan gillar da aka yiwa jikan Manzon Allah, Imam Husaini (A.S) a filin Karbala a shekara ta 61 bayan hijiran Manzon Allah (S).

bana ma yankin Kaduna Suleja Sun gudanar da wannan Tattaki, dan raya al'amarin aba Abdallah Imam Hussain (AS), an fara tattakin ne da misalin karfe 10:00pm na safiyar yau Asabar 19-10-2019 dai dai da 20-2-1441AH,

Idan mai karatu bai manta ba, an fara wannan Tattaki ne tin a ranar Alhamis da ya gabata, inda aka fara daga yankunan Fambeguwa da kuma Kaduna,  Sannan da safiyar jiya jumma’a yankin Kano, gadar gayan. Ya yin da yau Asabar a ka kammala a Suleja.

Isiya-Sy
Kaduna Press