Shugaban kwamitin tsaron na 'yan Majalisar Najeriya ya ce kudin da aka ware na yaki da kungiyar boko haram a kasafin kudin kasar ya kasa.

Yayin da yake amsa tambayoyin manema labarai a jiya laraba, shugaban kwamitin tsaro na 'yan Majalisar Najeriya Mohammed Ali Ndume ya ce binciken da kwamitin ya gudanar kan abubuwan dake gudana a yankin ya nuna cewa ta'addancin kungiyar boko haram a kasar da ma sauran kasashen yankin ya karu, kuma har yanzu kungiyar boko haram din na nan da karfinta, don haka kudin da aka warewa bangaren tsaro na yaki da kungiyar boko haram a kasafin kudin kasar na shekara 2020 mai zuwa ba zai bayar da sakamako mai kyau ba.

Ndume ya ce naira biliyan daya ta yi kadan a yaki da kungiyar boko haram, ko da wannan kudi an ware shi ne domin biyawa sojojin Najeriya bukatunsu, to wannan kudi ya yi kadan, don haka ya kamata mu san cewa muna cikin yaki ne, don haka a ganinmu kudin da aka ware na yaki da kungiyar boko haram a kwasafin kudin kasa na shekarar 2020 ya yi kadan kuma ba zai bayar da sakamakon da ake bukata ba.