Rahotanni daga Najeriya na cewa an rufe makarantar sakandare ta garin Dapchi dake jihar Yobe a arewa maso gabashin kasar.

Bayanai sun ce an dau wannan matakin ne saboda fargabar hare-haren kungiyar Boko Haram a yankin.

Hukumar makarantar da kungiyar iyayen daliban makarantar ne suka ba da sanarwar rufe makarantar na wani lokaci.

Sai dai ma'aikatar ilimi ta jihar Yobe, ta shaida cewa a hukumance ba a rufe makarantar ba, amma suna da masaniya akan matakin da hukumar makarantar da iyayen daliban suka dauka.

A karshen makon da ya gabata ne wasu da ake zargin 'yan kungiyar Boko Haram, suka kai hari a garin Babban Gida da ke makwabtaka da garin Dapchin.

Idan ana tune a watan Fabrairun 2018 ne wasu 'yan kungiyar Boko Haram suka sace dalibai mata sama da 100 a yankin.