Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

Nan da wasu makwanni Iran za ta fara aiki da wani bangare na cibiyar Nukiliya ta Arak


Shugaban hukumar makamashin Nukiliya ta kasar Iran Ali Akbar Salihi ne ya bayyana haka a jiya Litinin, yana mai cewa; Za a bude bangare na biyu ne na wannan cibiyar

Ali Akbar Salihi wanda ya gabatar da taron manema labaru ya kara da cewa; Mun yi matukar kokarinmu kuma a bisa umarnin jagoran juyin musulunci na cigaba da gudanar da bincike na ilimi, don haka ne mu ka amince da aiki da sharuddan dakatar da aiki na wani kayyadajjen lokaci.
Shugaban hukumar makamashin Nukiliyar ta Iran ya ce; Nan da makwanni biyu zuwa uku ne za a fara aiki da sabbin bututun tace sanadarin uranium na zamani, wanda kuma hakan bai sabawa yarjejeniyar Nukiliya ba.

Salihi ya yi ishara da cewa a karkashin yarjejeniya da akwai ayoyin doka da su ka bayar da damar daukar wannan irin mataki idan wani bangare ya ki aiki da yarjejeniyar.

Post a Comment

0 Comments

Close Menu