Babban sakataren kungiyar Hizbullah ya bayyana cewa, ana shirya wata makarkashiya da nufin haifar da yakin basasa a Lebanon.

Tashar Almanar ta bayar da rahoton cewa, a lokacin da yake gabatar da wani jawabi dangane da abubuwan da suke faruwa a Lebanon, Sayyid Hassan Nasrullah ya bayyana cewa a halin yanzu akwai hannu kasashen duniya da kuma na yankin gabas ta tsakiya a cikin abin da yake faruwa.

Sayyid Nasrullah ya ce, a lokacin da aka fara bore kasa da makonni biyu da suka gabata, jama’ar kasar ce suke bukatar a janye harajin da aka dora kan wasu abubuwa, kamar yadda kuma suke bukatar a kawo karshen barna da dukiyar kasa, da hukunta masu hannu wajen yin barnar.

Haka nan kuma jama’a suna bukatar a gudanar da sauye-sauye a cikin harkokin siyasar kasar, ta hanyar canja salon siyasa a kasar daga bangaranci na addini da kabilanci zuwa dimukradiyya zalla.

Ya ce dukaknin abubuwan da jama’a suke bukata hakkinsu kuma dole ne a saurare su kuma a dauki matakin yin gyara, kuma a wani mutum ne ya shirya haka ko yake jagorantar jama’a kan hakan ba, jama’a ne da da kansu suka bukaci hakan, kuma kungiyar Hizbullah tana goyon bayansu kan hakan.

Sayyid Nasrallah ya ce amma a halin yanzu akwai tabbatattun dalilai kan cewa gangamin da jama’a suke yi ba shi ne irin wanda aka fara da farko ba, domin yanzu wasu sun shiga cikin lamarin domin karkata gangamin jama’a zuwa nasu bukatun na siyasa, kuma akwai kasashe da suke daukar nauyin abin a yanzu, wanda kuma ga dukkanin alamu ana shirin yin amfani da hakan wajen haifar da mummunan yakin basasa ne a kasar ta Lebanon, wanda hakan ba maslaha ce ga kowa ba a kasar.

Ya ce yana kiran dukkanin magoya bayan gwagwarmayar kasar da su janye daga wuraren da ake gudanar da gangami a kasar.