Firai ministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya sanar da gazawarsa ta kafa gwamnati bayan ya shafe makonni yana zawarci kananan jam'iyyun kasar.
Yanzu damar ta koma ga babban abokin hamayyarsa Benny Gantz - amma shi ma zai fuskanci matsalolin da Mista Netanyahu ya shafe makonni yana kokawa da su, kamr yadda za ku ji a rahoton da Sani Aliyu ya hada mana.

Tun bayan da aka bayyana sakamakon zabe zagaye na biyu, ta bayyana Firai minista Benjamin Netanyahu ba zai iya kafa gwamnati ba.

Amma ya kafe wajen neman wata kafa na tsawon makonni, wanda kawo yanzu babu wani abin da ya sauya.

Ba zai kuma iya hada kan kujeru 61 a majalisar kasar ba. Wannan ne ya sa ya fitar da wani bidiyo wanda a cikinsa yake sukar Benny Gantz, wanda shi ne babban abokin adawarsa na siyasa da kan bashi hadin kai.

Shi dai Mista Gantz na jagorancin wata hadar jam'iyyu ne masu sassaucin ra'ayi,

kuma wannan dama ce a gare shi ya hada gwamnatin hadin gwuiwa tun da Mista Netanyahu ya gaza.

Amma shi ma yana fuskantar matsallolin da suka hana Mista Netanyahun kafa gwamanti - wato rashin isassun 'yan majalisa da za su ba shi rinjaye a majalisa.

Shugaban kasar ta Isra'ila ya bayar da wata shawara mai neman manyan jam'iyyun biyu su kafa gwamnati, wanda zai ba Mista Gantz ikon zama jagorar gwamantin, inda shi kuma Mista Netanyahu zai zama Firai minista amam na jeka na yi ka.

Sai dai yawancin 'yan Isra'ila na ganin dole ne a sake fafatawa a rumfunan zabe - a karo na uku kenan - idan ana son fitar da jam'iyya daya da za ta jagoranci kasar.